Makarfi Ya koma aiki a Sakateriyar PDP

Makarfi Ya koma aiki a Sakateriyar PDP

- A yammacin Laraba ne Sanata Ahmed Makarfi, ya koma aiki a sakateriyar PDP dake Gidan Wadata a birnin tarayya dake Abuja

- makarfi ya nua cewa zartarwar kotun kolin nasarace ga kowanna dan jam'iyyar ta PDP ba ga bangare daya ba

Ciyaman, Na gaba daya Na Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sanata. Ahmed Makarfi, ya koma aiki a sakateriyar PDP dake Gidan Wadata a Abuja a yammacin ranar Laraba, bayan zartarwar da kotu tayi na karbe shugabancin kungiyar daga hannun Sanata Ali Modu Sheriff.

Makarfi ya isa sakateriyar ne tareda tawagarsa da wasu daga manya-manya daga jam'iyyar a wasu yan mintina bayan zartarwar kotun koli a hukuncin nata na nuna rashin ingantuwar sherriff a matsayin shugaban jam'iyyar da da kotun patakwal tayi a da.

Makarfi Ya koma aiki a Sakateriyar PDP

Makarfi Ya koma aiki a Sakateriyar PDP

Manya-manyan jam'iyyar da suka halarci gurin kamar yarda NAIJ.com ta ruwaito sun kunshi Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti,Mataimakin shugaban Majalisar zartarwa, Sanata. Ike Ekweremadu, da wasu tsofaffin ministocin jam'iyyar.

A daga jawabansa a gidan na Wadata ga wasu daga taron mutane masu sauraronsa, makarfi ya nua cewa zartarwar kotun kolin nasarace ga kowanna dan jam'iyyar ta PDP ba ga bangare daya ba.

Ya kara da cewa gwagwarmayar da wasu daga shuwagabannin jam'iyyar sukayitayi a kotu kokarine na tabbatar da kyautatuwar siyasa a kasa baki daya.

KU KARANTA: Shirin yiwa Sanata Dino Melaye kiranye: Hukumar INEC ta dan ja baya kadan

Sanata Makarfi ya mika hannun gaisuwa mai dauke da ma'anar "ku taho mu tafi tare" ga bangaren jagorancin Sanata Sheriff da yunkurin sulhu a bisa adalci ga bangarorin.

Makarfi ya sake karawa da cewa kwamitin lura da jam'iyyar zasu tuntubi manyan gabobi daga jam'iyyar don samar da karin hanyoyin cigba ga jam'iyyar

Mai bada shawara ga jam'iyyar, Honorable Dave Iorhemba, a nakaltowar NAIJ.com ya shedawa manema labarai cewa hukuncin kotun nasara ne ba ga jam'iyyar kadai ba amma ga kasa baki daya.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa/

Kalli Bidiyo: mai dauke da bayanan Mukaddasin shugaban kasa gameda yakin biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel