Jaridar Financial Times da ke Landan tace Buhari ya gaza ciyar da tattalin arzikin Najeriya gaba

Jaridar Financial Times da ke Landan tace Buhari ya gaza ciyar da tattalin arzikin Najeriya gaba

- Ana fuskantar matsi na tattalin arziki a Najeriya

- Wasu na ganin gwamnatin Buhari ita ta kara zafafa talaucin

- Jaridar FT tace Buhari ya gaza

Jaridar Financial Times tace shugaba Buhari ya gaza wajen iyar da tattalin arzikin Najeriya gaba, inda tace ya gagara yin hakan a shekaru biyu da yake mulki, banda jinya da yawo kasashe babu abinda gwamnatin tayi.

Wakilin Jaridar na sashen Afirka, David Pilling, yace tattalin arzikin Najeriya a shekarun nan kamar wata matacciyar mage ce da aka jika da kunu aka kuma jehodaga dogon bene, sannan ake tsammanin zata diro da kafafuwanta.

Jaridar Financial Times da ke Landan tace Buhari ya gaza ciyar da tattalin arzikin Najeriya gaba

Jaridar Financial Times da ke Landan tace Buhari ya gaza ciyar da tattalin arzikin Najeriya gaba

Hasashen habakar tattalin arzikin bana na 2.5% ma yake ba lallai a kai shi ba, a bara dai tattalin arzikin Najeriyar ya habaka ne da kashi daya bisa dari kacal.

Wannan gazawa ce a cewar jardar FT, duba da yadda a da ake samun habakar tattalin arzikin Najeriya a da na kashi 7 cikin dari.

KU KARANTA KUMA: Buhari ne zai lashe zaben shugaban Kasa, a 2019

A cewar jaridar dai, farashin mai ya dan gyaru, haka ma kuma danyen man da kasar ke fitar wa ya habaka zuwa ganga miliyan kusan biyu a bara, bayan da a da ake iya itar da ganga miliyan daya kacal, amma duk da haka shugaba Buhari bai iya ya juyo akalar tattalin arzikin kasar ba.

Banda haka ma dai, jaridar tace shugaba Buhari yana jinya ne da yawon kasashen waje wanda hakan ya haifar da gibin shugabanci a kasar mai yawan jama'a miliyan kusan dari biyu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel