Buhari ba zai dawo ya karasa mulkinsa ba, inji FFK

Buhari ba zai dawo ya karasa mulkinsa ba, inji FFK

- Fani-Femi Kayode yace yana da tabbas cewa Buhari bazai dawo ba

- Yace a sako shugaba Buhari a hoton bidiyo idan ba tsoro ba

- Yace jinyar shugaban ta kawo karshen mulkinsa

Femi Fani Kayode tsohon ministan Obasanjo, wanda ke ffuskantar dauri kan zargin cin hanci da rashawa, ya ce yana da tabbacin cewa shugaba Buhari bazai dawo Najeriya ba, ya kuma karyata FArfesa Yemi Osinbajo da cewa wai Buhari na nan yana samun sauki.

'Ina sanar da 'yan Najeriya cewa babu wani warkewa da Buhari ke yi, kuma babu wani sauki da ya samu, hasali ma, ba zai taba dawowa Najeriya ya ci gaba da mulki ba' inji Fani Kayoden a shafinsa na fesbuk.

Buhari ba zai dawo ya karasa mulkinsa ba, inji FFK

Buhari ba zai dawo ya karasa mulkinsa ba, inji FFK

A yau da safennan ne dai dan PDPn yayi wannan ffuruci, inda ya yi kira ga Yemi Osinbajo da ya deba yaudarar 'yan Najeriya, wai in ma ba tsoro ba, su fito su nuna wa duniya shugaba Buharin.

Ya ce lallai mu 'yan Najeriya mun damu da lafiyar shugaba Buhari, kuma mun matsu mu saka shi a ido, don wannan hakkin mu ne tunda mun zabe shi a matsayin shugaba.

KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa tace Buhari ne zai lashe zaben 2019

'Wai shin yana ma raye kuwa? Yana iya magana? Yana iya gane mutane? Yana da cikakken hankali da rashin mantuwa? Su fito su fada mana gaskiya, kuma su bayyana inda sugaban namu yake.' ya kara da cewa.

A shekarar 2014 da 2015 dai, FFK yayi kaurin suna wajen caccakar jam'iyyar da ya baro ta APC, inda ya kira ta jam'iyyar Musulmai kuma jam'iyya mai kishin arewa kadai.

A yanzu dai watanni biyu sun shude tun tafiyar shugaba Buhari asibiti a kasar Ingila, kuma tun sallah ba'a kara jin muryarsa ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel