Gwamnati za ta share wa jihohi 15 da ambaliyar ruwa ta shafa hawaye da biliyan 1.6

Gwamnati za ta share wa jihohi 15 da ambaliyar ruwa ta shafa hawaye da biliyan 1.6

- Gwamnatin tarayya za ta tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihohi 15

- Osinbajo ya umurni minstan kudi da ta gaggauta fitar da naira biliyan 1.6 domin a rabawa jihohin da ke fama da ambaliyar ruwa

- Mai magana da yawun shugaban kasa ya ce tallafin kudin zai taimaka wa mazauna jihohin

Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya umurni ministar kudi, Kemi Adeosun da ta gaggauta fitar da naira biliyan 1.6 daga babban bankin kasar, CBN ta rabawa jihohi 15 da ambaliyar ruwa na kwanan na ta shafa.

Jihohin da suke fama da ambaliyar ruwan sun hada da; Ekiti, Osun, Akwa Ibom, Kebbi, Neja, Kwara, Ebonyi, Enugu, Abiya, Oyo, Legas, Filato, Sakkwato, Edo da Bayelsa.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan da kammala taron majalisar zartarwa.

Gwamnati zata share wa jihohi 15 da ambaliyar ruwa ta shafa hawaye da biliyan 1.6

Ambaliyar ruwa a wasu jihohin Najerya

Adesina ya ce wannan tallafin za ta taimaka wa mazauna jihohin da ambaliyar ruwan ta shafa.

KU KARANTA: Najeriya baza ta iya kara ciwo bashi a waje ba, inji Kemi Adeosun, ministar kudi

Osinbajo ya ce an umurni ministan kudi da ta mikawa hukumar agajin gaggawa ta kasa (NEMA) kudaden kai tsaye domin fara aiki nan take.

Yawan ruwan sama a kwanakin nan ta yi sanadiyar ambaliyar ruwa a wasu sassan jihohin Legas da Niger inda aka yi asarar rayuka da dumbin dukiyoyi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel