Rikicin PDP: Sheriff yayi Magana akan hunkuncin da kotun koli na kasa ta zartar

Rikicin PDP: Sheriff yayi Magana akan hunkuncin da kotun koli na kasa ta zartar

-Ina taya Makarfi murna

-Jami'yya zata cigaba da damawa da Sherrif

-Abin da ke gaban mu yanzu shine kwace mulki a hannun APC

Shugaban da aka sauke na jami’yyar peoples democratic party(PDP) senata Ali Modu Sherrif, yayi Magana akan shariar da kotun koli ta zartar.

A ranar laraba da ta gabata kotu ta fitar da tsohon gwamnan jihar Borno daga ofis bayan rikicin shugabancin jami’yan, da ya dauki lokacin mai tsawo ana gwabzawa.

Manyan jigogin jami’yo na adawa sun nuna farincikin su akan wannan sharia. Su nuna cewa hakan nasara ne ga dimokuradiyyan Najeriya.

Rikicin PDP: Sheriff yayi Magana akan hunkuncin da kotun koli na kasa ta zartar	.

Rikicin PDP: Sheriff yayi Magana akan hunkuncin da kotun koli na kasa ta zartar .

Wannan nasarar baban alama ne da ya nuna za mu iya kwace mulki a hannun jami’iyyar All progressive congress(APC) a 2019.

KU KARANTA: Babu mai tausayin talaka cikin shugabannin Najeriya, inji Balarabe Musa

Gwamanan jihar River Nyesom Wike yace Sheriff zai bi umarnin kotu, kuma za aci gaba da damawa dashi a matsayin dan jami’yan. Ya fadi haka ne bayan kotu ta zartar da shari'an sauke Sherrif.

Sheriff yayi Magana a shafin sa na tuwita @sen AliSheriff cewa” kotun koli tayi Magana, ina taya Makarfi murna.

Sherrif yakara da cewa wannan lokaci ne da zasu hada kawunan su dan cigaban PDP. Kuma su tunkari abin dake gaban mu shine kwace mulki a hannun APC.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel