An ceto wata mata da aka kulle a daki na tsahon shekaru 15

An ceto wata mata da aka kulle a daki na tsahon shekaru 15

Jami'an ‘yan sandan na yankin Goa dake yammacin kasar Indiya ta sanar da kubutar da wata dattajiwan mata da ‘yan uwanta suka kange ta a daki har na tsahon shekaru goma sha biyar.

Matar da aka ambata da suna Sunita Verlekar dai yanzu haka tana da shekarun 50 a duniya.

Da yake bayani ga manema labarai akan al’amarin, wani jami’in dan sanda SP Karthip Kashyap ya bayyana cewa sun samutsegumi a kan matar ne daga kungiyar kare hakkin mata da ta shahara a kasar mai suna Bailancho Saad.

A cewar shi “bayan mun samu labarin sai muka aika tawagar ‘yan sanda mata gidan da aka garkame matar wanda ke a kauyen Candolini inda suka je suka kubutar da ita”

An ceto wata mata da aka kulle a daki na tsahon shekaru 15

An ceto wata mata da aka kulle a daki na tsahon shekaru 15 Hoto: Alummata

Bisa ga rahoto, matar ta dawo gida ne daga Mumbai shekaru goma sha biyar da suka shige bayan da ta gano cewa mutumin da take tare da shi ya na da wata matar.

KU KARANTA KUMA: Caraf an fara kame masu kazamin lodi a manyan titunan Tarayya

Sanadiyar faruwan hakan ne ta fara wasu bakin halaye wanda shine ya sa ‘yan uwan ta suka kange ta a daki har na tsahon wannan lokaci, abinci ma ta taga suke bata.

Jami'an sun ce zuwa yanzu basuyi ram da kowa a kan al'amarin ba amma ana nan ana gudanar da bincike a kan al’amarin.

Ita kuwa matar an mika ta ga asibitin kwakwalwa da gyara halaye mallakar gwamnatin jihar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel