Siyasa: Atiku na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP

Siyasa: Atiku na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP

- Ana sa ran Alhaji Atiku Abubakar zai sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP

- Wannan shawara ta biyo bayan nasarar sanata Ahmed Makarfi a kotun koli

- Yanzu haka an kafa kwamiti na musamman domin ganin Atiku ya samu tikitin takara a shekarar 2019

Wasu rahotanni da suka fito bayan da kotun koli na kasa ta tabbatar da sanata Ahmed Makarfi a matsayin ainihin shugaban jam’iyyar PDP na bayyana cewa Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa a karkashin mulkin jam’iyyar PDP na shirin sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Za a tuna cewa a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli ne kotu ta kawo karshen rikicin cikin gida da jam'iyyar PDP tayi fama dashi na tsowan lokaci, sanata Ahmed Makarfi tabattacen shugaban jam'iyyar na kasa na shirin tarbar tsohon mataimakin shugaban kasar zuwa cikin jam'iyyar yanzu haka.

A cewar jaridar Sarauniya, yanzu haka an kafa kwamiti na musamman wanda ta fara aiki domin ganin Atiku ya samu tikitin takara a zabe mai zuwa ta shekara 2019 a karkashin jam'iyyar PDP da zaran ya amince ya koma.

Siyasa: Atiku na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa PDP

Jam'iyyar adawa, PDP

A shekarar 2011 tsohon mataimakin shugaban kasar ya shiga fafatawa wajen neman tikitin zaya takara da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Abubuwa 4 da ka iya faruwa a yanzu da Makarfi ya yi nasara a shugabancin PDP

Hausawa sun ce da tsohon zuma ake magani, ko Atike zai amince ya koma PDP....

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel