Hukumar JAMB ta fara saida fom din shiga jami'a na 2017

Hukumar JAMB ta fara saida fom din shiga jami'a na 2017

- Hukumar Jamb ta fara saida fom din DE

- Hukumar tace a bankuna za'aje a siya

- Hukumar dai ita ke da alhakin shiraya jarabawar shiga jami'a

Hukumar nan mai alhakin yin jarabawa da kuma samar wa da dubban masu karatu a kasar nan guraben karatu a makarantun gaba da Sakandire watau The Joint Admission and Matriculation Board (JAMB) a turance ta bayyana cewa ta fara saida fom din shiga jami'a ga na DE ga mai so.

Wannan dai yana kunshe ne cikin wata sanarwar da jami'in hulda da jama'a na hukumar Mr. Fabian Benjamin ya fitar ya kuma rabawa manema labari.

Hukumar JAMB ta fara saida fom din shiga jami'a na 2017

Hukumar JAMB ta fara saida fom din shiga jami'a na 2017

NAIJ.com dai ta samu labarin cewa kwanan nan ne dai aka kammala yin jarabar shiga jami'ar ga daruruwan dubban matasan dake da bukata a dukkan fadin kasar nan.

Haka ma dai sanarwar ta bayyana cewa siyen fom din a bankunan kasar za'a yi shi kamar dai yadda aka saba a duk shekara.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel