Buhari ya samu lafiyar da zai iya mulkar Najeriya har nan da shekara 15 - Majiya

Buhari ya samu lafiyar da zai iya mulkar Najeriya har nan da shekara 15 - Majiya

- An ruwaito shugaba Buhari na samun sauki

- Shugaban dai ance zai ma iya mulkin Najeriya shekara 15

- A jiya ma dai Osinbajo ya kai mashi ziyara

Wata majiyar mu da bamu gama tantance sahihancin labarin ta ba ta bayyana cewa Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari fa ya samu lafiya fiye da duk yadda yan kasar ke tunani.

Majiyar tamu haka zalika ta sake tabbatar da cewa nan ba da dadewa shugaban zai dawo kasar domin ci gaba daga inda ya tsaya.

Buhari ya samu lafiyar da zai iya mulkar Najeriya har nan da shekara 15 - Majiya

Buhari ya samu lafiyar da zai iya mulkar Najeriya har nan da shekara 15 - Majiya

NAIJ.com dai ta samu labarin cewa majiyar tamu ta ci gaba da cewa yanzu haka shugaban zai iya ci gaba da mulkar kasar har nan da shekaru 15 masu zuwa ba ma 2 ba ko shekara 6.

Mai karatu dai zai iya tunawa cewa a jiya da dare ne dai mukaddashin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya shilla zuwa kasar Birtaniya inda Shugaba Buhari ke jinya ya kuma gana da shi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel