Wata sabuwa! Kamar Dino Melaye, an fara shirin yiwa Saraki kiranye

Wata sabuwa! Kamar Dino Melaye, an fara shirin yiwa Saraki kiranye

- Saraki ya shiga taskon siyasa a gida

- Matasa sun sha alwashin yi masa kiranye

- Yanzu haka yaron sa Dino Melaye na fuskantar wannan kalubalen

Yanzu haka dai al'amurra sun fara dagulewa a can jihar Kwara dake arewa ta tsakiyar Najeriya inda wasu matasa suka daura damarar lallai sai sun maido shugaban majalisar dattijai gida.

Matasan dai da dattijai in asalin mazabar Bukola Saraki din nne wadanda suka taru suka kafa wata kungiya mai suna 'Dole ne jihar Kwara ta canja' watau 'Kwara Must Change' kenan a turance.

Wata sabuwa! Kamar Dino Melaye, an fara shirin yiwa Saraki kiranye

Wata sabuwa! Kamar Dino Melaye, an fara shirin yiwa Saraki kiranye

NAIJ.com ta tsinkayi shugaban wannan kungiya mai suna Abdulrazaq O Hamzat yana mai cewa yana ba dukkan daukacin yan Najeriya hakuri game da zaben tumun daren da suka yi.

Amma a cewar sa, sun yi da-na-sanin yin hakan su kansu kuma yanzu haka sun daura damarar ganin ya dawo gida kamar yadda ake shirin yi wa babban yaron sa a majalisar watau Sanata Dino Melaye.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel