Yan majalisar wakilai sun ba Osinbajo kwana 7 ya nada sabbin ministoci ko ya gane kuren sa

Yan majalisar wakilai sun ba Osinbajo kwana 7 ya nada sabbin ministoci ko ya gane kuren sa

- Sabon rikici na shirin ballewa a majalisa

- Majalisar wakillai ta ba Osinbajo wa'adi

- Majalisar tace ya tabbata ya cika wa'adin cikin kwana 7

Wata sabuwar hatsaniya dake son tasowa daga majalisar tarayya tsakanin yan majalisar da kuma fadar shugaban kasar ta Najeriya da yanzu haka take karkashin ikon Farfesa Osinbajo tana dada kunno kai.

A jiya ne dai majalisar ta bawa Farfesa Osinbajo wa'adin kwana 7 ya tabbatar da ya rantsar da sabbin ministocin da aka rigaya aka tantanci kusan watanni biyu kenan da suka gabata a cikin watan Mayu.

Yan majalisar wakilai sun ba Osinbajo kwana 7 ya nada sabbin ministoci ko ya gane kuren sa

Yan majalisar wakilai sun ba Osinbajo kwana 7 ya nada sabbin ministoci ko ya gane kuren sa

NAIJ.com ta samu labarin cewa yan majalisu daga jihar Kogi da kuma Gombe wanda kuma daman daga nan ne ministocin suka fito sune suka gabatar da kudurin hakan a zauren majalisar kafin daga baya kuma majalisar ta amince da hakan.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa ministan dake wakiltar jihar Kogi yayi hatsari ne ya mutu yayin da ita kuma ministar dake wakiltar jihar Gombe Amina Muhammad ta samu ci gaba ne inda yanzu haka take da babban matsayi a majalisar dinkin duniya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel