Ruwa yayi mummunar barna a jihar Katsina, gidaje sama da 100 sun rushe

Ruwa yayi mummunar barna a jihar Katsina, gidaje sama da 100 sun rushe

- Ruwa yayi gyara a jihar Katsina

- Mamakon ruwan sama ya rushe gidaje sama 100

- Har yanzu ba'san ainihin asarar da aka tafka ba

Wani mamakon ruwan sama da aka samu mai karfin gaske a karamar hukumar Kaita dake a jihar Katsina yayi mummunar barna a karshen satin da ya gabata kamar yadda rahotannin mu ke nuni.

Kamfanin jaridar Vanguard dai ya ruwaito cewa kimanin gidaje sama 100 ne suka rushe sannan kuma munane sama da 2000 suka rasa matsuguni a karamar hukumar inda al'amarin ya faru.

Ruwa yayi mummunar barna a jihar Katsina, gidaje sama da 100 sun rushe

Ruwa yayi mummunar barna a jihar Katsina, gidaje sama da 100 sun rushe

NAIJ.com ta samu labarin kuma cewa hukumar nan dake bada agajin gaugawa ta jihar watau SEMA ta tabbatar da ukuwar lamarin inda mai magana da yawun hukumar ya tabbatar wa da majiyar tamu afkuwar hakan.

Sai dai kuma jami'in hulda da jama'a na hukumar Umar Muhammad ya bayyana cewa kawo yanzu babu wani takamaiman kiyasin barnan da ruwar yayi ba.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel