Za mu gyara kasar nan cikin shekara daya da rabi – Osinbajo

Za mu gyara kasar nan cikin shekara daya da rabi – Osinbajo

- Osinbajo yace Gwamnatin su za ta gyara kasar nan cikin shekara guda da rabi

- Mukaddashin Shugaban kasar Osinnajo ya nemi masu jari a kasa su dafa masu

- Amma Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun tace Najeriya na cikin damuwa

Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kara jaddada kudurin Gwamnatin su na gyara kasar nan cikin watanni 18. Farfesan ya bayyana wannan ne jiya a wani taro da aka yi a Fadar Shugaban kasa.

Za mu gyara kasar nan cikin shekara daya da rabi – Osinbajo

Osinbajo yayi wa ‘Yan Najeriya babban alkawari

A taro kun ji cewa Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun tace Najeriya ba ta isa ta karbi bashi ba don Najeriya za ta biya bashin sama da Miliyan $480 da ake bin ta a halin yanzu daga kasafin kudin kasar wanda ba zai kai labari ba.

KU KARANTA : Buhari ya kusa dawowa Inji Osinbajo

Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya nemi masu hannun jari da sauran ’Yan kasuwa da su sa hannu wajen ganin kasar ta canza nan da shekara guda da rabi. Osinbajo yace wannan Gwamnati a shirya take wajen hakan.

Kun ji Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana yadda su kayi da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Landan inda su ka hadu a jiya da dare.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

A raba Najeriya ko ayi garambawul?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel