Zaben 2019: Da wa za'a kara ne? PDP ko APC?

Zaben 2019: Da wa za'a kara ne? PDP ko APC?

- Kotu ta yanke hukunci kan rikicin PDP

- Zabukan 2019 suna kara matsowa

- Ko shugaba Buhari zai iya tsayawa takara

A yau ne aka karashe karar da jam'iyyar PDP bangaren Ali Modu Sheriff ta kai kan batun shugabancin jam'iyyar, wanda suka shafe shekaru biyu suna yi.

An dai sami tsaiko sosai wajen baiwa jam'iyyar APC adawa mai ma'ana, domin kuwa ita kanta jam'iyyar PDPn a wannan shekara biyu babu wata alkibla da ta sa a gaba, banda rigima da surutai, da ma batun sace sace da almundahana a lokacin mulkinsu.

Zaben 2019: Da wa za'a kara ne? PDP ko APC?

Zaben 2019: Da wa za'a kara ne? PDP ko APC?

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ne zai lashe zabukan 2019

A yanzu dai a cikin banan nan za'a fara jin duriyar 'yan takara, sannan kuma a cikin badi ne za'a gama zabukan cikin gida, inda a karshen badin hukumar zabe zata gudanar da duka zabuka.

Akwai gwamnoni da yawa da suke son zarcewa, amma kuma a rigar Buhari suka sami tsallake hararar talakawansu.

Ko shugaba Buharin zai sake takara? In kuma ba zayyi ba, wanene manyan jamiyyu zasu tsayar, a PDp da APC? Akwai dai mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo, akwai kuma Alh. Atiku Abubakar, ga kuma Injiniya Rabi'u Kwankwaso.

A cikin APC din dai akwai Bukola Saraki da Bola Tinubu, Rochas Okorocha da ma Orji Kalu na Abiya.

A PDP kuma akwai Sule Lamido, Malam Ibrahim Shekarau, Ali Sheriff, Ayo Fayose, da ma Donald Duke.

A jihohi kuma, da yawa daga gwamnoni baza su sami goyon bayan talakawansu ba, saboda yawan karuwar talauci da aikin yi, da kuma kunnen uwar shegu da 'yan siyasa suke yi musu bayan zabuka a 2015.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel