Rikicin cikin gida a APC ta Kaduna ya kazanta

Rikicin cikin gida a APC ta Kaduna ya kazanta

- Wata bangare na jami’iyyar APC a jihar Kaduna tace gwamnan baya tabuka aikin komai

- Bangaren da suka ware suna zargin El-Rufai da rashin gudanar da ayyukansa ta hanya sahihiya

- Yan APC Akida sun ce mutanen jihar sun shiga wahala tun lokacin da El Rufai ya dare kujeran mulki

Wasu yan jami’iyyar APC a Kaduna da suka ware kansu daga sauran yan jami’iyar sun bada kuri’ar rashin amincewa a bias yadda gwamna El Rufai yake gudanar da mulki a jihar.

Mutanen da ke kiran kansu APC Akida sun bada wannan sanarwan ne ga Jaridar Premium times ta bakin shugaban kwamiti na yan APC Akida Mr. Maitaimaki Maiyashi

Rikicin cikin gida a APC ta Kaduna ya kazanta

Rikicin cikin gida a APC ta Kaduna ya kazanta

Shugaban kwamitin yan wariyan, Mr Maiyashi yace: “An ruguza jami’iyyar da gangar har ta kai matsayin da bata iya tabuka komi.

Ana sa sojojin baka suna cin mutuncin duk wanda ya bada shawarar da zata amfani jama’a.

“Shawarar kawai da ake dauka shine na wasu baren kwararu da aka dauko daga wajen jihar wanda basu ma fahimci yadda jihar take ba da matsalolin ta.”

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ne zai lashe zabukan 2019, inji Minista

Mr Maiyashi yace addamar da aikin ruwan Zaria da aka yi a 29 ga watan Mayun shekara 2017 kawai “zamba ce cikin aminci."

“Muna tambaya, ina hikima cikin musgunawa yan kasuwan Barci kawai don za’a gina Kasuwan zamani irin na Dubai?

“Ina hikimar siyar da kadarorin gwamnati? Ini hikimar sauke hakimai da masu sama da 4000?

“Ina hikimar karbo bashi daga bankin duniya a yayinda bashi yayi ma jihar katutu?."

Yan APC Akidar sun hada da Isa Ashiru, dan takarar gwamnar jami’iyyar da El Rufai ya kada shi a zaben fida gwani a shekara 2015; Senata Shehu sani; Yaro Makama; Sule Buba; Ibrahim Iko da kuma shugaban gidan talabijin da rediyo na Liberty, Tijjani Ramalan.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel