Dalilin da yasa har yanzu Najeriya ke samar da wutar lantarki ga Nijar da Jamhuriyar Benin – Inji Fashola

Dalilin da yasa har yanzu Najeriya ke samar da wutar lantarki ga Nijar da Jamhuriyar Benin – Inji Fashola

- Fashola ya bayyana dalilin da yasa kasar Nijar da Benin suka fi Najeriya samu wutar lantarki

- Minitan ya tabbatar cewa kasashen biyu sun fi jin dadin wutar lantarki fiye da Najeriya

- Fashola ya ce akwai yarjejeniyar cewa kasashen biyu ba zasu iya yi wani sabon dam a kogin Kainji Dam wanda ke samar wa Najeriya wuta ba

Ministan wutar lantarki, ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola a ranar Talata, 11 ga watan Yuli ya bayyana dalilin da yasa kasar ke cigaba da samar da wutar lantarki zuwa kasar Jamhuriyar Benin da Nijar.

Fashola ya ce kasashen biyu sun fi jin dadin wutar lantarki fiye da Najeriya.

NAIJ.com ta ruwaito cewa ministan ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin da yake magana a wani taron gwamnatin tarayya wato Quarterly Presidential Business Forum wanda aka gabatar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Dalilin da yasa har yanzu Najeriya ke samar da wutar lantarki ga Nijar da Jamhuriyar Benin – Inji Fashola

Mukaddashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Babatunde Fashola, Kemi Deosun da wasu jami'an gwamnati a fadan shugaban kasa a Abuja

Ya ce dole ne a samar wa kasashen biyu wadatan wutar lantarki saboda yarjejeniyar cewa ba zasu iya yi wani sabon dam a kogin Kainji Dam wanda ke samar wa Najeriya wutar lantarki ta hanyar ruwa.

KU KARANTA: Shugabanci Na Gari: Wani shugaban Arewa ya caccaki Abdulsalam cewa sune suka lalata Najeriya

Taron wanda ta samu halartar wakilan tawagar masu kula da tattalin arziki a gwamnatin shugaba Buhari a karkashin jagorancin mukaddashin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel