2019: Mu zamu kafa gwamnati bayan zabe - Ayo Fayose

2019: Mu zamu kafa gwamnati bayan zabe - Ayo Fayose

- An gama shari'ar shugabancin PDP a kotun koli

- Ayo Fayose yace su Buhari su fara hada kayansu

- An baiwa Makarfi jam'iyyar PDP

Bayan yanke hukuncin da kotun koli ta yi kan batun shugabancin PDP, gwamna Ayo Fayose na Ekiti yace lokaci ne na dinke baraka a cikin gida, inda ya ce jam'iyyar APC ta hada komatsan ta su bar gidan gwamnati, domin wai a 2019, sune zasu kafa gwamnati.

A yau Laraba ne dai kotu ta mikawa bangaren Ahmed Makari na Kaduna shugabancin PDP, a inda manyan jam'iyyar suka ce kowa yazo a hada kai a gyara jam'iyyar.

2019: Mu zamu kafa gwamnati bayan zabe - Ayo Fayose

2019: Mu zamu kafa gwamnati bayan zabe - Ayo Fayose

Shekaru biyu dai ana gwabzawa tsakanin bangarorin biyu inda kowanne ya garzaya kotu suke ta kokarin karbe iko da jam'iyyar, wannan dai ya zamo wani abin dariya da ya dauki hankalin 'yan Najeriya tun bayan faduwarsu zabe.

KU KARANTA KUMA: Wasu musulmai sun yi auren jinsi daya

Manyan dattijan jam'iyyar dai sun kasa shawo kan lamarin amma a yanzu ga dukkan alamu zasu iya shiga zabukan 2019 a badi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel