Dalilin da ya sa kotu ta daga shari’ar Nnamdi Kanu zuwa watan Oktoba

Dalilin da ya sa kotu ta daga shari’ar Nnamdi Kanu zuwa watan Oktoba

Wata babban kotun tarayya dake babban birnin tarayya Abuja ta daga sauraron shari’ar da take yin a shugaban kungiyar masu fafutukar neman Biyafara, Nnamdi Kanu zuwa ranar 17 ga watan Oktoba.

A cewar kotun ta dage karar ne saboda tana cikin hutu a yanzu haka.

A yau ne ya kamata a koma kotu domin ci gaba da saurarar karar tun bayan da aka bayar da belin Kanu.

Kanu tare da wasu mutane uku David Nwawuisi, Benjamin Madubugwu da Chidiebere Onwudiwe na fusktankar tuhuma akan cin amanar kasa.

Dalilin da ya sa kotu ta daga shari’ar Nnamdi Kanu zuwa watan Oktoba

Dalilin da ya sa kotu ta daga shari’ar Nnamdi Kanu zuwa watan Oktoba

A watan Afrilu, alkalin kotun, mai shari’a Binta Nyako ta bayar da belin shugaban kungiyar ta IPOB bisa wasu tsauraran sharudda.

KU KARANTA KUMA: 2019: Mu zamu kafa gwamnati bayan zabe - Ayo Fayose

Sai dai tun lokacin da ya samu ‘yanci, Kanu ture wadannan sharuddan a kefe, inda ya ke ci gaba da gudanar da ayyukansa ba tare da la’akari ko duba da su ba.

Kungiyar IPOB kuwa na ci gaba da kafewa akan cewa Kanu bai keta ko daya daga cikin sharuddan kotun ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel