Abubuwa 4 da ka iya faruwa a yanzu da Makarfi ya yi nasara a shugabancin PDP

Abubuwa 4 da ka iya faruwa a yanzu da Makarfi ya yi nasara a shugabancin PDP

- Bangaren Makarfi ta yi nasarar rikicin shugabanci dake jam’iyyar ta PDP

- Kotun koli ta nemi Sheriff ya biya tara

- Jam’iyyar na iya fuskantar wasu canje-chanje bayan shugabancin

Da alama rikicin jam’iyyar PDP ta zo karshe bayan kotun koli a Abuja ta yanke hukunci a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli.

An kaddamar da bangaren Ahmed Makarfi na PDP a matsayin ainahin shugaban jam’iyyar PDP a kasar.

Jam’iyyar ta fara rikici tun a shekarar 2015, bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kayar da dan takarar ta.

Abubuwa 4 da ka iya faruwa a yanzu da Makarfi ya yi nasara a shugabancin PDP

Abubuwa 4 da ka iya faruwa a yanzu da Makarfi ya yi nasara a shugabancin PDP

A halin yanzu Jam’iyyar na iya fuskantar wasu canje-chanje bayan shugabancin ta ya dawo hannun Ahmed Makarfi.

KU KARANTA KUMA: Sababbin kyawawan hotunan Halima da Zahra Buhari

1. ‘Yan siyasar da sukayi barazanar barin jam’iyyar da ma wadanda suka bari na iya dawowa.

2. Sheriff na iya kafa sabuwar jam’iyya wanda zai koma tare da magoya bayansa

3. Jam’iyyar APC na iya fuskantar barazana, kamar yadda wasu da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC sakamakon rikicin jam’iyyar na iya komawa jam’iyyarsu ta da tunda komai ya daidaita a yanzu

4. Ahmed Makarfi na iya canja wasu al’amuran jam’iyyar da Ali Modu Sheriff ya shimfida a yanzu da ragamar jam’iyyar ta dawo hannun sa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel