Giyan Mulki: Ali Modu Sherriff ya nuna yaranta karara da hadamar sa a fili – Kotun Koli

Giyan Mulki: Ali Modu Sherriff ya nuna yaranta karara da hadamar sa a fili – Kotun Koli

- Alkalan kotun koli guda uku sun kalubalanci Ali Modu Sheriff da nuna maitar san shugabancin PDP

- Sun ce canje-canjen kotu da yake yi domin samun nasara kira ne bayan hari

- An nemi Sheriff ya biya naira dubu dari biyu da hamsin

- Magoya bayan Makarfi na nan sun shirya liyafa sakamakon nasara da sukayi a kotu

A shari’ar da Kotun Koli ta yanke yau Larabar, 12 ga watan Yuli a babban birnin tarayya Abuja tsakanin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bangaren Ali Modu Sherrif da na Makarfi, Alkalai uku da suka yanke hukuncin sun bayyana cewa babu shakka Ali Modu Sherrif ya nuna maitarsa a fili domin zama shugaban jam’iyyar ta PDP.

Alkali Rhodes Vivour da ya karanto hukuncin kotun ya ce abinda Modu Sherriff ya yi na shiga kotuna daban-daban don samun nasara akan wannan shari’a tada kura ce kawai sannan kotun da suka bashi nasara a wancan lokaci sun sunyi hukunci a cikin duhu wato kenan sun tafka gagarumin kuskure.

Giyan Mulki: Ali Modu Sherriff ya nuna yaranta karara da hadamar sa a fili – Kotun Koli

Ali Modu Sherriff ya nuna yaranta karara da hadamar sa a fili inji Kotun Koli Hoto: Premium Times

KU KARANTA KUMA: Ka ji kudin da kwastam ta samu cikin ‘yan watanni

Ya ce a dalilin haka Ali Sherrif zai biya naira dubu dari biyu da hamsin (250,000).

Tuni dai liyafa ya barke a hedikwatan jam’iyyar ta PDP dake babban birnin tarayya Abuja inda magoya bayan Ahmad Makarfi ke ta taka rawa domin nuna farin ciki da murna kan wannan hukuncin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel