Shugabanci Na Gari: Wani shugaban Arewa ya caccaki Abdulsalam cewa sune suka lalata Najeriya

Shugabanci Na Gari: Wani shugaban Arewa ya caccaki Abdulsalam cewa sune suka lalata Najeriya

- Dr. Junaid Mohammed ya kalubalanci kwamitin Abdulsalam cewa sojoji na cikin shugannin da suka lalata Najeriya

- Mohammed ya ce shugabannin soja masu son kai sune suka jefa kasar Najeriya a cikin mawuyacin halin

- Muhammed yace ya amince cewa wasu batattu ‘yan siyasa suka lalata kasar

Wani dan majalisa a jamhuriya ta biyu, Dr. Junaid Mohammed ya mayar da martani kan bayanin kwamitin samar da zaman lafiya ta kasa a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Alhaji Abdulsalami Abubakar.

Mohammed, wani jigo dan siyasa a jamhuriya ta biyu ya ce, shugabannin soja masu son kai sune suka jefa kasar Najeriya a cikin mawuyacin halin da take yau.

A cewar shi: “ Bai kamata a dora laifin a kan ‘yan siyasa kadai ba, tsohon shugannin na mulkin soja suma sun kasance masu laifi”.

Shugabanci Na Gari: Wani shugaban Arewa ya caccaki Abdulsalam cewa sune suka lalata Najeriya

Dr. Junaid Mohammed, wani jigo dan siyasa a jamhuriya ta biyu

Kwamitin samar da zaman lafiya ta kasa a zamanta a ranar Talata, 11 ga watan Yuli ta zargi ‘yan siyasan kasar cewa rashin shugabanci na gari yayi sanadiyar kiran da wasu ke yi na raba kasar.

KU KARANTA: Najeriya ta yi sa'an samu shugaba irin Buhari – Inji Mukaddashin shugaban kasa

Mohammed ya ci gaba da cewa: "Na amince da wannan kalaman kwamitin Abdusalam cewa da dama wasu batattu ‘yan siyasa suka lalata kasar, kuma suka aikata manyan zalunci ga dimokuradiyya”.

“ Duk da haka, ba daidai ba ne a zargi ‘yan siyasa kawai. Zan iya ce ba tare da tsoron musu cewa sojoji suna da hannu a cikin lalata kasar. " A cewar Dr. Junaid Mohammed

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel