Najeriya baza ta iya kara ciwo bashi a waje ba, inji Kemi Adeosun, ministar kudi

Najeriya baza ta iya kara ciwo bashi a waje ba, inji Kemi Adeosun, ministar kudi

- Tattalin arzikin Najeriya yana ta tambal tambal

- An baiwa Najeriya bashi ta ki karba

- Kemi Adeosun tace sai dai a nemi kudi a cikin gida

Ministar Kudi, kemi Adeosun, tayi gargadin cewa Najeriya baza ta iya kara ciwo bashi ta zuba a kasafin kudi ba.

Ta koka kan karancin kasafin kudi bazai wadatar da aikata muhimman ayyuka ba a Kasar, sai dai a nemi hanyar samun kudi a cikin gida da za a zuba a kasafin kudi.

Najeriya ta tsaida bashin da ta shirya ciyowa daga Bankin Duniya na $2 biliyan. Adeosun ta bayar da shawarar Najeriya bazata sake ciyo bashi ba. Mai da hankali akan haraji shi ne dai-dai, duk da shi baikai karbar bashi saurin tafi da Kasa ba. Amma hakan zai hana Kasar fadawa tarkon bashi.

Najeriya baza ta iya kara ciwo bashi a waje ba, inji Kemi Adeosun, ministar kudi

Najeriya baza ta iya kara ciwo bashi a waje ba, inji Kemi Adeosun, ministar kudi

Arzikin Kasar nan ya koma baya a cikin shekarun nan. Kasafin kudinmu yayi kadan, albashi kawai muke iya biya, baya isa a gudanar da muhimman ayyuka. Kasafin kudinmu 6% ne a kwatankwacin GDP, bai kai na takwarorinmu ba. Yayi kasa sosai idan aka kwatanta da na wasu kasashen nahiyar Afrika, a cikin Kasashen Duniya kuwa Najeriya tana cikin na kasa-kasa.

Babu isashen kudi a Gwamnati da zai isa Gwamnati tayi abun da ake bukata. Na san zakuce don masu sace kudin Gwamnati ne, amma koda za a hada da kudaden da ake sacewa ba zai isa ba. Karancin biyan haraji da mutane suke yi ya haifar da karanci a kasafin kudinmu.

KU KARANTA KUMA: Albaghdadi ya rasu a Sham

Kwatankwacin GDP na Kasar mu bai kai na Kasashen da suka cigaba ba. In muna so muga mun cigaba dai-dau da Kasashen da suka cigaba sai munyi koyi da irin abubuwan da suke yi.

Kasar nan zata cigaba ne in har Kwatankwacin GDP zai zo daya da Kasashen da suka cigaba. Muna kokarin muga mun daidaita kasarmu da Kasashen da suka cigaba.

Mukaddashin shugaban Kasa, Yemi osinbajo ya jaddada wajibcin yankunan kanfanin sana’o'i masu zaman kansu ganin sun sa hannu don cigaban kasa. Yana tabbatar da samun sauyi a tsarin kasafi a watanni masu zuwa. Ya kuma kara da bayanin yadda mafi yawan kamfani a Kasar India suke samarwa da kansu wutar lantarki hakan shi yasa kasar cigaba ta fuskar kalubalen da take fuskanta.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel