Batutuwan da na gana da Shugaba Buhari a kansu a ziyara ta Ingila - Yemi Osinbajo

Batutuwan da na gana da Shugaba Buhari a kansu a ziyara ta Ingila - Yemi Osinbajo

- Osinbajo ya ziyarci Buhari a Ingila

- Osinbajo ya shaida Shugaba Buhari na dawowa bada jimawa ba

- Sun tattauna akan batutuwa daban-daban

Mukaddashin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya tafi Ingila a ranar Talata don duba lafiyar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Muhammadu Buhari ya shafe sama da wata biyu da barin Najeriya don duba lafiyarsa a Ingila. Wannan shine Tafiyar Buhari zuwa Ingila na biyu a cikin shekararnan don duba lafiyarsa.

Batutuwan da na gana da Shugaba Buhari a kansu a ziyara ta ta Ingila, Yemi Osinbajo

Batutuwan da na gana da Shugaba Buhari a kansu a ziyara ta ta Ingila, Yemi Osinbajo

NAIJ.com ta samu labari daga wata majiya cewa Buhari ne ya bukaci zuwan Osinbajo domin su tattaunawa akan wasu batutuwa. Zuwan Osinbajo Ingila don duba lafiyar Buhari ne da kuma tattaunawa akan cigaban da aka samu a Kasa tun bayan tafiyarsa.

Tattaunawar da suka yi ya shafe tsawon awa daya. Osinbajo ya shaida sun tattaunna akan abubuwa da dama.

KU KARANTA KUMA: Ta Buhari ta kare - inji Fayose

Osinbajo yace: "Buhari yana murmurewa sosai yana kuma samun sauki, yana nan dawowa bada jimawa ba." Ya shaida sauraron dawowar Buhar kwanannan don yana samun lafiya sosai.

Laoulu Akande, kakakin Farfesa Osinbajo ya rubuta a shafinsa na tuwita ‘Osinbajo zai gana da Buhari a Ingila a yau kuma zai dawo da zarar ya kammala. Ya sake shaida mana ta shafinsa dawowar Osinbajo wanda zai jagoranci taro da ministoci a Abuja da karfe 11 na safiyar Laraba’.

Mukaddashin Shugaban Kasa yace: "bamu yi magana akan rantsar da sabbin ministoci guda biyu daga Jahar Kogi da Gombe ba, wanda Majalisa ta tantance a watan Mayu."

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel