Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 6 (hotuna)

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 6 (hotuna)

Dakarun rundunar sojin Najeriya na birgediya 7 tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na kar ta kwana sun yi nasarar kakkabe ‘yan ta’adda dake zaune a kauyen Dawashi Gari, a wani yanki da ke iyakar tafkin Chadi da kasar Najeriya.

An samu labarin ne a cikin wata sanarwa da mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar soji, mukaddashin darakta kanal Timothy Antigha ya fitar wanda ke cewa a safiyar Talata 11 ga watan Yuli.

Dakarun sojin sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 4 a yayin da sauran suka gudu suka bar baburan su wanda aka gano aka lalata.

KU KARANTA KUMA: Ka ji kudin da kwastam ta samu cikin ‘yan watanni

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 6 (hotuna)

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda kauyen Dawashi Gari Hoto: Alummata

KU KARANTA KUMA: Ka ji kudin da kwastam ta samu cikin ‘yan watanni

Har ila yau, a duk cikin yunkurin da ake yi wajen ganin an kawo karshen ta’addanci a yankin arewa maso gabashin Najeriya, sojojin bataliya 145 birged 5, da jami’an tsaro na kar ta kwana sun samu nasaran barrantar mayakan kungiyar ‘yan ta’adda daga kauyukan Gashigar, Asaga, Bukarti da sauran kauyukan da ke kusa da su.

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 6 (hotuna)

Sun kwato wasu kayayyaki daga 'yan ta'addan Hoto: Alummata

A wannan hali ne dakarun suka hadu da wasu ‘yan ta’adda a kauyen Kanama inda suka fafata da su suka kashe 2 daga cikin sun sannan kuma suka kama 2 tare da amshe makaman su da baburan su.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel