Najeriya ta yi sa'an samu shugaba irin Buhari – Inji Mukaddashin shugaban kasa

Najeriya ta yi sa'an samu shugaba irin Buhari – Inji Mukaddashin shugaban kasa

- Osinbajo ya ce kasar Najeriya ta yi sa’a wajen samu shugaba irin Buhari

- Osinbajo ya bayyana haka ga ‘yan jarida a Abuja

- Ya ce gwamnati zata yi iya kokarinta a kan alkawuranta ga ‘yan Najeriya

Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a ranar Talata, 11 ga watan Yuli ya ce, kasar Najeriya ta yi gagarumin sa’a wajen samu shugaba mai saukin ganewa irin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Osinbajo ya bayyana haka ne yayin da yake magana a wani taron gwamnatin tarayya wato Quarterly Presidential Business Forum wanda aka gabatar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

NAIJ.com ta ruwaito cewa jiya Talata ne Osinbajo ya yi ziyarar farko ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a Landan inda suka gana na sa’o’i daya. Ya ce shugaba Buhari ya samu sauki sosai fiye da ake sammani kuma zai dawo kwana nan.

Najeriya ta yi sa'an samu shugaba kamar Buhari – Inji Mukaddashin shugaban kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo

KU KARANTA: Daga dawowa? Osinbajo zai jagoranci ganawar majalisar zantarwa a yau

Mukaddashin shugaban kasa ya ce, gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Buhari zata yi iya kokarinta a kan alkawuranta ga ‘yan Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel