YANZU-YANZU: Shugaba Buhari zai dawo kwanan nan – Inji Osinbajo

YANZU-YANZU: Shugaba Buhari zai dawo kwanan nan – Inji Osinbajo

- Osinbajo ya tabbatar da cewa shugaba Buhari zai dawo kwanan nan

- Osinbajo ya ce, ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Landan

- Mukaddashin shugaban kasa ya ce shugaba Buhari ya samu sauki sosai fiye da ake sammani

Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ji sauki sosai kuma jim kadan zai dawo don ya ci gaba da shugabancin kasar.

Mista Osinbajo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a babban birnin kasar, Abuja.

Mukaddashin shugaban kasar ya ce, ya hadu da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Landan a ranar Talata, 11 ga watan Yuli. Wannan ne ziyarar farkon na Osinbajo ga shugaba Buhari tun da shugaban ya tashi zuwa kasar Birtaniya a watan Mayu da ta gabata don duba lafiyarsa.

YANZU-YANZU: Shugaba Buhari zai dawo kwanan nan – Inji Osinbajo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo

KU KARANTA: YANZU-YANZU: Osinbajo yayi zaman sa’a 1 da Buhari, amma ya ki furuci akan ganawar

Osinbajo ya ce: “ NA gana da shugaba Muhammadu Buhari a Landan, ya samu sauki sosai fiye da kuke sammani kuma fara’arsa na nan yanda kuka sani”. A cewar Mukaddashin shugaban kasar".

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel