Naira Tiriliyan daya ce muke nema don harkokin tsaro, amma biliyan arba'in kawai aka bamu a kasafin kudin bana, inji Insifeta Janar

Naira Tiriliyan daya ce muke nema don harkokin tsaro, amma biliyan arba'in kawai aka bamu a kasafin kudin bana, inji Insifeta Janar

- Ana samun matsalolin harkar tsaro a Najeriya

- Hukumar yansanda bata da kudaden da take bukata

- An sami karuwar sabbin laifuka da a da babu

Insifecta Janar na 'yan sanda, Ibrahim Idris, yace rashin kudaden gudanarwa na daga cikin mishkiloli da ke takure hukumar sa wajen iya yaki da laifuka da tabbatar da doka.

Shugaban 'yan sanda, ya bada kiyasin kudin da hukumar 'yan-sanda ke bukata akan naira tiriliya N1.13, inda yace biliyan 36 kawai ya samu a kasafin kudin bana, Naira tiriliyan dai sai an hada biliyan sau dubu ake samuta.

Naira Tiriliyan daya ce muke nema don harkokin tsaro, amma biliyan arba'in kawai aka bamu a kasafin kudin bana, inji Insifeta Janar

Naira Tiriliyan daya ce muke nema don harkokin tsaro, amma biliyan arba'in kawai aka bamu a kasafin kudin bana, inji Insifeta Janar

A cewarsa, kusan biliyan 200 suke bukata domin gyara ofisoshi da bariki na ma'aikata, a waje daya kuma ko man fetur da motocinsu 14,000 zasu sha, kusan na biliyan talatin ne.

Akwai karin kudi na sayen makamai, babura, karnuka, dawaki, da ma tafiyar da ofis, kari da kudaden da binciken laifuka ke cinye wa, inda ya bada kiyasi a kan kusan biliyan 200.

KU KARANTA: Kotun Koli ta mikawa Makarfi jam'iyyar PDP

A cewarsa, idan ana son hukuma mai karfi, wadda zata iya tafiyar da sikinta cikin tsari, dole ne a bada hadin kai da kudaden da suke bukata, kuma ma dai, yace akwai sabbin laifuka da barayi ke yi wadanda a da ba'a saba ganinsu ba.

A cewar sa dai, sai da kudade ne za'a iya koyar da ma'aikata sabbin hanyoyi na zamani domin fada da laifukan zamani.

Karen bana dai, dama ance shine maganin zomon bana.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel