Shugabancin PDP: Ali Modu Sheriff ya ki halartar zaman kotun da ya kada shi

Shugabancin PDP: Ali Modu Sheriff ya ki halartar zaman kotun da ya kada shi

-Ali Sheriff ya sha kasa a yau a kotu

- Kotun koli ta mika wa Makari jam'iyyar PDP

- An shafe shekaru ana rikici a PDP

A da dai muddin aka ce ana batun shugabancin PDP, zaka sami kotu makil da magoya bayan Ali Modu Sherif tsohon gwamnan jihar Borno, amma a yau da safe a kotu, babu wanda ya ziyarci kotun cikin magoya bayansa na gaba gaba.

Shugabancin PDP: Ali Modu Sheriff ya ki halartar zaman kotun da ya kada shi

Shugabancin PDP: Ali Modu Sheriff ya ki halartar zaman kotun da ya kada shi

Shima dai Ali Sheriff din bai halarci zaman kotun na yau ba, zama wanda ya fara daga karfe 8, kuma tuni alkalan kotun kolin suka yanke hukunci suka mika wa sashen tsohon gwamnan Kaduna Ahmed Makarfi jam'iyyar.

A yau din dai da safe, gaggan jam'iyyar da suka halarci zaman sun hada da Olisa Metuh, Uche Secondus da ma gwamnan Ribas Nyesom Wike.

KARANTA KUMA: Kotun Koli ta mika wa Makarfi jam'iyyar PDP

Sai kuma Emeka Ihedioha tsohon mataimakin kakakin majalisar tarayya, da kuma dan karadi Ayo Fayose na jihar Ekiti. Sai Farfesa Jeri Gana da Zainab Maina, da Obi Nwabueze.

A baya dai dukkan wadannan mutane sun sha alwashin barin PDP muddin Ali Sheriff ya ci galaba a kotu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel