Uwa ta siyar da jaririnta dan watanni biyu don ta siya mota a Anambra (hoto)

Uwa ta siyar da jaririnta dan watanni biyu don ta siya mota a Anambra (hoto)

- An kama wata mata bayan ta siyar da jaririnta mai watanni biyu a duniya

- An tattaro cewa ta hada kai da kawarta ne gurin siyar da jaririn

An kama wata uwa mai shekaru 24 da aka ambata da suna Oluchi Emeobi kan laifin siyar da jaririnta mai watanni biyu a jihar Anambra don ta siya mota.

A cewa jaridar The Punch, an kama matashiyar a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli, bayan ta hada kai da kawarta Nchedoch Richard gurin siyar da jaririn nata.

An tattaro cewa kawayen biyu sun siyar da jaririn mai watanni biyu a duniya ga wata mata da aka fi sani da First Lady.

Uwa ta siyar da jaririnta dan watanni biyu don ta siya mota a Anambra (hoto)

Uwa ta siyar da jaririnta dan watanni biyu don ta siya mota a Anambra Hoto: Ladun Laidi

Garba Umar kwamishinan ýan sanda na jihar ya bayyana cewa Emeobi ta zo ofishin ýan sanda don kai karar cewa an sace mata danta.

KU KARANTA KUMA: Daga dawowa? Osinbajo zai jagoranci ganawar majalisar zantarwa a yauDaga dawowa? Osinbajo zai jagoranci ganawar majalisar zantarwa a yau

Kwamishinan ya bayyana cewa an kwato kudi N250,000 da wani mota da ta siya da kudin da ta siyar da jaririn bayan an kama ta.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel