ETISALAT: Karshen kamfanin sadarwar ya zo

ETISALAT: Karshen kamfanin sadarwar ya zo

- Abinda ke faruwa a kamfanin Etisalat

- Etisalat sun yi jinjina ga ‘yan kasuwar su

Kamfanin hanyar sadarwa na, Emerging Markets telecommunication Services Ltd (EMTS) wanda aka fi sani da Etisalat, bayyana cewa har yanzu suna nan da wannan sunan na su, sanadiyar cire hannun da (UAE) kasashen larabawa na gabas suka yi na wani babban kaso daga kamfanin.

Mataimakin shugaban kamfanin sadarwar Ibrahim Dikko, ya yi bayanin a ranar da ta gabata cewa, suna da masaniya a kan cire hannun da EMTS suka yi daga Etisalat Najeriya, kuma har yanzu suna nan da sunan na sun a Etisalat Najeriya.

ETISALAT: Karshen kamfanin sadarwar ya zo

ETISALAT: Karshen kamfanin sadarwar ya zo

Ya bayyana cewa “har yanzu akwai birbishin hadin gwiwar tsakanin su, kuma suna nan da cigaba da tattaunawa da akan yadda za a kawo karshen wannan al’amari.

KU KARANTA: Wani dalibin koyan aikin soja ya gamu da azal

Yace shekaru 9 da kafuwar wannan kamfani a kasar nan, sun ta ka rawar gani kuma sun bada gudunmawa a wajen cigaban kasar ta hanyar inganta sadarwa, kawo aikin yi ga al’umma, habaka kasuwancin ta hanyar saukakawa ‘yan kasuwa.

Ya kara da cewa, duk da wannan abin a gani a fada da suka yi a kasar nan, suna yin jinjina da godiya ga wadanda suke kasuwanci da su da kuma bada hakurin jajircewar su a kan cigaban kamfanin na sadarwa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel