Sanya hijabi ne hanya mafi sauki na yi wa mutane fashi – matashin da aka kama ya tona asiri

Sanya hijabi ne hanya mafi sauki na yi wa mutane fashi – matashin da aka kama ya tona asiri

- An kama wani dan Najeriya mai matsakaicin shekaru bayan ya badda kamanni don yi wa mutane fashi

- An kama mutumin ne a garin Minna

Wani dan Najeriya mai suna Ibrahim Shuaibu ya tona asiri kan dalilin sa na yin shigar mata tare da sanya hijabi gurin yiwa mutane fashi.

Mutumin mai matsakaicin shekaru ya fito daga Tudun Nasira a garin Minna, jihar Niger. Ta kwabe ma Shuaibu lokacin da ýan sanda suka kama shi kan laifin satar wayoyi da sauran abubuwa daga mazauna unguwanni.

Shuaibu ya yi rashin saá lokacin da yayi ma wani mutumi mai suna Adamu Usman fashin kudi da waya a hanyar Gbednaye, Maitumbi.

Sanya hijabi ne hanya mafi sauki na yi wa mutane fashi – matashin da aka kama ya tona asiri

Ibrahim Shuaibu matashi dake ma mutane fashi ta hanyar sanya hijabi Hoto: Punch.

An rahoto cewa barawon ya ji ma wanda yayi ma fashi raunuka a hannu da wuka yayinda yayi yunkurin yi masa fashi. Da aka turke shi, mai laifin ya tona asirin cewa ya kwashe tsawon shekaru biyar yana fashi a Maitumbi.

KU KARANTA KUMA: Daga dawowa? Osinbajo zai jagoranci ganawar majalisar zantarwa a yau

“Yi ma mutane fashi ya zamo dabiá na wanda na kasa dainawa. Wasu lokutan, ina shiga irin na masa kafin nayi fashi amma a yanzu, don tsoron karda a gane ni da sauri, sai na koma ssanya hijabi kafin nayi ko wani fashi."

Matashin ya bayyana cewa rashin aikin yi ne ya sanya shi fadawa wannan harka. Da aka tambaye shi dalilin sa na shigar mata kafin ya yi fashi, ya ce mutane basa saurin zargin mata da fashi.

“Sanya hijabi ya fi komai sauki wajen fashi domin da wuya mutane su zargi mace da fashi da makami,” inji shi.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel