Kasar nan zata samu cigaba a tattalin arzikinta nan da watanni 18 - Osinbanjo

Kasar nan zata samu cigaba a tattalin arzikinta nan da watanni 18 - Osinbanjo

- Mukaddashin shugaban kasa ya yi kira ga yan kasuwa da su taimaka

- Adeosun ta ce bai dace Najeriya ta cigba da karbo bashi ba

- Abubuwa za su yi kyawu nan gaba

Yiwuwar haka zai kasance idan yan kasuwa sun hada gwiwa da gwamnatin tarayya dan daga darajar tartalin arzikin kasar.

Mukkadashin shugaban kasan yayi wannan kira a taron kasuwanci na tsakiyan shekara a Abuja, inda manyan yan kasuwa suka halarta.

Ya yi kira ga yan kasuwanni da su yi kokarin ganin cewa an samu nasara wajen cigaban tatttalin arzikin kasan, duk da cewa an samu gajeruwan matsala wajen fitar kasafin kudin shekara.

Kasanan zata samu cigaba a tartalin arzikinta nan da wata 18- Osinbanjo

Osinbajo tare da Adeosun

Minister tartalin arziki Kemi Adeosun tace dole a zafafa a wajen karban haraji dan hada kudaden kasafin kudi. Bai dace kasanan ta cigaba da karfo bashi ba.

KU KARANTA KUMA: Sababbin kyawawan hotunan Halima da Zahra Buhari

Ta yi kira ga yan kasuwa da su dauki daman da gwamanati ta basu na hadin gwiwa wajen yin kasuwanci da yin abu da yakamata dan samu nasara.

A maganarsa a ranar bikin damokradiya ya ce tattalin arzikin kasar shine baban kalubale ga mulkin shugaba Buhari. Kuma gwmanati na iya kokarin ganin cewa an samu saukin al’amarin. Saboda munga tasirin da hakan yayi a rayuwar yan Najeriya.

Mukkadashin shugaban kasan ya nuna cewa yan Najeriya sunyi hakuri a yan shekarun da suka gabata. Amma Yayi alwashin cewa abubuwa zasu suyi kyau nan gaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel