An kai ma dan takaran jam’iyyar PDP hari a jihar Benue.

An kai ma dan takaran jam’iyyar PDP hari a jihar Benue.

-Yan ta’adan sun zo a cikin motocin guda uku kiran bas

-Da kyar na sha da rai na

-Karnnukan APC suka kai mun hari.

Yan tasha sun kai ma dan takaran jam’iyyar PDP a zaben shekaran 2015 da ta gabata Hon. Tarzoor hari dake Yandev karamar hukuman Gboko d ke jihar Benue.

Wa’ayanda suke wajen lokacin da aika-aikan ya faru sun shaida ma manema labarai cewa yan ta’adan sun zo a cikin motocin guda uku kiran bas wajen wani gidan cin abinci dake bayan Aperan Orshi makarantan noma , Hon Tazoor malami ne mai karatarwa anan kuma nan yake shakatawa da abokansa.

Shaidu sun ba da labarin cewa, an ji wa mutane da dayawa rauni a hari da akai ma Hon Tarzoor, magoya bayansa sa ne suka ceci yaruwansa yayin da suka boye shi har sai da yan ta’adan suka wuce.

An kai ma dan takaran jam’iyyar PDP hari a jihar Benue.

Hon Terhermeen Tarzoor

Da aka same shi dan tabbatar da gaskiyan labarin” Tazoor ya bayyana cewa hakan ya faru da shine yayin da yashiga makarantar saboda gayyatan da abokansa mallamai a suka yi.

Ku Karanta:hHukumar Kastam ta samu makudan kudi cikin kankanin lokaci

“ Yan ta’aadan wa’ yanda nake sa ran karannukan jam’iyyar APC ne, su kai mun hari. Bayan na iso wajen da kamar minti goma, sai gasu a cikin motoci guda uku. Suka ci mutunci na da na abokaina da duk wani mutum dake wajen.

Dake kyar na sha da raina wasu mutane suka gudu dani wajen boya. Bayan haka yan ta’adan suka ci gaba da duka mutane da lalata musu dukuyoyi. Jama’a da dama sun ji raunaka a harin .

Ina kira da magoya bayana da kada su dauki doka a hanun su, suyi hakuri. Kuma Ina kira ga manyan yan siyasa jihar da su zama masu son zaman lafiya, kada su zama masu son tashin hankali.

Shugaban jam,iyya APC na jihar Hon Abba Yaro ya maida martini cewa shi bai san haka yafaru dashi ba kuma matasan APC masu tarbiyya ne ba za su taba aikata haka ba.

Da aka tuntubi Jami’an yan sandan jihar sun tabbatar da haka ya faru ama suna kan binciken al’amarin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel