Tofa: Ana yunkurin yin juyin mulki a Najeriya

Tofa: Ana yunkurin yin juyin mulki a Najeriya

- Mulkin shugaba Buhari ya fuskanci kalubale

- Ana yunkurin yin juyin mulki a kasar nan

- Kungiyar Sojoji da leken asiri sun yi gargadi a kan yunkurin.

Wata kungiyar sojoji da leken asiri sun bayyanawa Sahara reporters da su gargadi gwamnatin Najeriya a kan yunkurin juyin mulki da wadansu daga cikin kusoshin gwamnatin Najeriya su ke kokarin yi mata.

Kungiyar sun yi gargadi a kan cewa wadansu manyan gwamnatin Najeriya wadanda suke aiki karkashin gudanarwar Sanata Bukola Saraki da shugaban ma'aikata na Buhari Abba Kyari, su na kokarin yin juyin mulki a kasar nan.

Sahara reporters sun ruwaito cewa wadannan masu kwadayin karbar mulkin. Najeriya su na yunkurin ne ganin yadda shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake fama da rashin lafiya kuma su ka sa yin tawwakalin dawowar sa.

Tofa: Ana yinkurin yin Juyin Mulki a Najeriya

Tofa: Ana yinkurin yin Juyin Mulki a Najeriya

Rahotanni daga kungiyar sun bayyana cewa irin wannan yanayi da ake ciki a Najeriya, irin shi ne ya faru a lokacin da marigayi Umaru Yar'adua yake mulkin kasar nan. Kungiyar sun bayyana cewa a lokacin da Yar'adua ya tafi kasar Saudiya don neman lafiya shi, irin haka ta faru na yunkurun Juyin mulki a kasar nan.

A lokacin shugaban sojan kasa na Najeriya Laftanar Janar Abdurrahman Dambazau, ya yi iya ka bakin kokarin shi na kafa dakarun tsaro da leken asiri a kan yunkurin da akayi na juyin mulkin shugaba Umaru, kuma ya gargadi mukaddashin shugaban kasa na lokacin, Goodluck Jonathan a kan cewa ya yi taka tsan-tsan.

KU KARANTA: Ka ji kudin da kwastam ta samu cikin 'yan watanni

Rahotanni sun bayyana cewa a watan Mayun shekarar nan, shugaban sojan kasa na yanzu, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi gargadin cewa ana yunkurin yin juyin mulki a kasar nan. Bayan wata biyu da yin wannan gargadin, ba bu mutum daya da aka kama da zargin yin juyin mulkin, daman an yi hakan ne domin masu yunkurin yin juyin mulkin sun san irin shirin da za su yi idan an yi kokarin hana su.

A ranar 3/Yuli/2017 ne a birnin tarayya, aka yi bikin kaddamar da wani littafi na Birgrdiya Janar Zakariyya Maimakari, hakan ya baiwa masu yunkurin yin juyin mulkin dama da su tattauna da juna a kan shirye shiryen da suke yi don ganin sun yi nasara.

Kungiyar suna gargadin mukaddashin shugaban kasa da ya lura kuma ya kiyaye a kan ganin haka bata faru ba, sa'annan kuma ya kafa wadanda yake ganin ya aminta dasu domin samun nasara a kan masu wannan yunkurin.

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel