Osinbajo zai fada ma ýan Najeriya sakamakon ganawarsa da shugaba Buhari - Akande

Osinbajo zai fada ma ýan Najeriya sakamakon ganawarsa da shugaba Buhari - Akande

- Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Landan a ranar Talata, 11 ga watan Yuli

- Tuni dai Osinbajo ya dawo kasar bayan ganawar

- Nan ba da jimawa ba zaá sanar wa jamaá dalilin ganawar a cewar fadar shugaban kasa

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai sanar da alúmmar kasar sakamakon ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Landan.

Mista Laolu Akande, babban mataimaki na musamman ga mukaddashin shugaban kasa a shafin zumunta da kafofin watsa labarai, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a daren ranar Talata, 11 ga watan Yuli bayan dawowar maigidansa kasar.

Ya bayyana ganawar a matsayin “ganawa mai kyau sosai.”

KU KARANTA KUMA: Daga dawowa? Osinbajo zai jagoranci ganawar majalisar zantarwa a yau

Osinbajo zai fada ma ýan Najeriya sakamakon ganawarsa da shugaba Buhari - Akande

A yayinda Osinbajo ya bar kasar Hoto daga: Aso Rock

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel