Tsohuwar Ministar kudin Najeriya ta kara samun matsayi

Tsohuwar Ministar kudin Najeriya ta kara samun matsayi

- Tsohuwar Ministar Najeriya ta kara samun matsayi a Duniya

- An kara nada ta Shugaban wata Kungiyar lafiya ta Bill Gates

- Wannan ne kusan karo na biyu da za tayi a wannan matsayi

Ministar kudin Najeriya a da lokacin Shugaba Jonathan da Obasanjo watau Ngozi Okonjo-Iweala ta kara samun matsayi a Duniya bayan an kara ba ta Shugabar Kungiyar GAVI ta su Bill Gates.

Tsohuwar Ministar kudin Najeriya ta kara samun matsayi

Hoton Tsohuwar Ministar kudin Ngozi Iweala

Wannan karo an kara nada Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin kujerar Shugabar wata Kungiyar kula da lafiyar Jama'a ta Attajirin Duniya Bill Gates da Mai Dakin sa Melinda Gates. Okonjo-Iweala za tayi shekara uku kan kujerar.

KU KARANTA : Osinbajo ya zura Landan ganin Buhari

Tsohuwar Ministar kudin Najeriya ta kara samun matsayi

Shugaba Buhari tare da Bill Gates

Kungiyar dai ta Duniya ta yabawa irin aikin da Okonjo tayi mata tun lokacin da aka nada ta a bara 2016. Dr. Okonjo-Iweala ta taimaka wajen tattali a harkar na riga-kafin yara da dama na Duniya. Iweala dai tayi Minista ba sau daya ba a Najeriya kuma ta san aikin na ta.

Ministar kudin Najeriya ta yanzu Kemi Adeosun tace Najeriya fa ba ta isa ta ci bashi ba don haka dole ta dage wajen neman kudi cikin gida.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Mai burodi ta zama mai kudi a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel