'Yan sanda su kama mutane 87 'yan kungiyar asiri da suka addabi mutane a yankin Ikorodu

'Yan sanda su kama mutane 87 'yan kungiyar asiri da suka addabi mutane a yankin Ikorodu

Kwamishinan 'Yan sanda ya ce wannan nasaran da aka samu, an same shi ne ta sanadiyar hadin gwuiwa da sauran jami'ar tsaro na ciki da waje da 'yan tsintiri na unguwanni da suka yi har aka kai ga kama su.

Sintirin da 'yan sanda Suke yi cikin dare ne aka samu nasaran kama mutane 87 'YAN kungiyar asiri a wani gida da ake zargin nan ne suke aikata tsafe-tsafensu, a Owutu da Odungunyan da ke karamar hukumar Ikorodu. Hukumar ta ba da shelar kama wadannan mutane da ake Zargin su da kashe mutane ta hangar amfani da tsafi sun hada da: Mashood (a.k.a Mosho), da Alfa (a.k.a king of boys), da Papa, da Fela, da Alakoto, da kuma Chukwudi.

Hukumar 'yan sanda ta jihar IkkoIkko, ta ba da sanarwar kama wadannan mutane 14 cikin gaggawa, sun hada da: Agbara O/c, Femi (a.k.a FM), da pencil, da Odidan, da Jeru, da Alien, da Bush, da Happiness, da Fagbo, da Junior, da Nuru, da kuma Jami'u.

Hukumar 'yan sanda sun yi kira ga wadanda make zargi da su kai Kansu da Kansu ofishin 'YAN sanda mafi kusa da su kafin fushin gwamnati ya fada Kansu. Sannan kuma ta nemi hadin kan mutane mazauna ikorodu, da su rika taimakawa jami'an tsaro da bayanai dangane da wadannan mutanen domin tabbatar da tsaro da zaman Lafiya a yankin.

'Yan sanda su kama mutane 87 'yan kungiyar asiri da suka addabi mutane a yankin Ikorodu

'Yan sanda su kama mutane 87 'yan kungiyar asiri da suka addabi mutane a yankin Ikorodu

An tura jami'an tsaro na musamman ne domin gano yadda aka kafa wannan kungiyar da kuma yadda suke gudanar da ayyukansu domin yakan su, musmman a wurare biyu masu Hatsarin gaske Owutu da Odungunyan. Hukumar 'yan sanda sun yi zama da Sojoji, da 'yan sanda na farin kaya da Malaman tsibbu, da bokaye da masu maganin gargajiya da 'YAN sintiri na unguwa da sauran jami'an tsarodomin dakile ko share wadannan kunyoyi a yankin.

Wakilin kwamishinan 'yan sanda na jihar legas Fatai Owoseni, DCP Imohimi Edgal ya gargadi malaman tsibbu da 'yan sintirin unguwa da masu maganin gargajiya da hukuncin da Suke yi na hukunta masu laifi nan take a gaban jama'a, kila haka zai hana wasu masu sha'awar shiga kungiyar su shiga. Jami'an tsaro na jihar ba za su lamunce ba.

KU KARANTA: Wani dalibin soja ya gamu da ajalinsa

DCP Edgal ya nemi hadin kan al'umma da su taimakawa jami'an tsaro da bayanai domin kawar da wadannan kungiyoyin da ke wannan yanki.

Kwamishinan 'yan sanda, ya samu ganawa da sarakunan gargajiya da hakimai da masu unguwanni da ke ikorodu. Domin tabbatar da an wasar da wadannan kungiyoyi da suka addabi jama'a, da Samar da ingantaccen tsaro a Ikorodu, jami'an tsaro sun hada kai da mataimakin kwamishinan 'yan sanda ACP Olatunji Dish, da Mukaddashin shugaban'yan sanda mai kula da yankin Ikorodu, da DPO da wasu manyan 'yan sandan.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel