KUMA! An kai harin kunar bakin wake Maiduguri

KUMA! An kai harin kunar bakin wake Maiduguri

Akalla mutane 11 ne suka hallaka a hare-haren Bam din da aka kai garin Maiduguri da daren jiya, Talata, 11 ga watan Yuli.

Wata majiyar jami’an tsaro wanda aka sakaye sunansa yace an kai hari na farko da na biyu ne misalign karfe 9:45 na dare garin Mulaikalmari.

Majiyar tace mutane 8 tare da yan kunar bakin waken ne suka hallaka a lokacin.

KUMA! An kai harin kunar bakin wake Maiduguri

KUMA! An kai harin kunar bakin wake Maiduguri

Kana kuma wasu 3 sun hallaka hari na uku da hudu da aka kawo yayinda mutane 5 suka jikkata a Polo-Sabon Garin Maiduguri.

“Dukkan hare-haren sun faru ne a wajen gari.”

KU KARANTA: Osinbajo ya tafi Landan ganawa da Buhari

Ya kara da cewa an kai wadanda suka jikkata asibitoci na musamman domin jinya.

Shugaban hukumar bada agaji na gaggawa na jihar, Alhaji Satomi Ahmed, wanda ya tabbatar da wannan hari yace an tura jami’ansa wajajen.

Kwamishanan yan sandan jihar Borno, Damian Chukwu, ya bayyanawa manema labarai cewa yawancin wadanda suka hallaka jami’an Civilian-JTF ne.

“12 daga cikinsu yan Civilian-JTF ne kuma sauran yaku bayi ne,”

“Sauran mutanen da suka mutu su taru wajen ta’aziyar jami’an Civilian-JTF 12 da aka far kashewa.”

Kakakin hukumar Civilian-JTF, Danbatta Bello, yace musamman yan Boko Haram din suka kai hari kan abokan aikinshi.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel