Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci Osinbajo ya rantsar da wasu sabbin ministocin Arewa 2

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci Osinbajo ya rantsar da wasu sabbin ministocin Arewa 2

- Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci a rantsar da ministoci biyu da majalisar dattijai ta tantance watannin baya

- Za a yi cikon gurubi da ministocin a jihgohin Kogi da Gombe

- Wani dan majalisar wakilai mai wakiltar jihar Kogi ya yi kiran a zaman majalisar

Majalisar wakilai a zaman ta na musamman ta kira mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da ya rantsar da ministoci biyu daga jihohin Kogi da kuma Gombe wandanda majalisar dattijai ta tattance watannin baya.

Dan majalisar wakilai, sunday Karimi Steve mai wakiltar jihar Kogi kuma dan jam’iyyar PDP ya yi wannan kira a zaman majalisar.

Za ku iya tuna cewa majalisar dattijai ta tantance Suleiman Hassan daga Gombe da kuma Ocheni Hassan Ikani daga Kogi a matsayin maye gurubin marigayi Barr. James Ocholi da kuma Ms Amina Muhammed bi da bi.

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci Osinbajo ya rantsar da wasu sabbin ministocin Arewa 2

Zauren majalisar wakilan Najeriya

KU KARANTA: Osinbajo ya amince da Alkalai 19 na Kotun Masana'antu

Duk da haka, bayan tantancewar majalisar dattijai, bangaren zartarwa ta kasa rantsar da ministocin da kuma sanya masu mukamai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel