Karda ki jefa Najeriya cikin rikici da furucin ki - Wani mutumi ya shawarci Aisha Buhari

Karda ki jefa Najeriya cikin rikici da furucin ki - Wani mutumi ya shawarci Aisha Buhari

- Wani dan Najeriya mai kula, Omololu Omotosho, ya gargadi uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari da ta dunga sanin irin furuci da zatayi game da ‘yan Najeriya

- An zargi Aisha Buhari da amfani da sunayen dabbobi gurin kiran ‘yan Najeriya yayinda take gode masu kan addu’o’in su ga mijinta

- Shugaban Muhammadu Buhari ya shafe kusan sama da watanni biyu a Landan inda yake jinya

A wani sako da aka aiko ga NAIJ.com, Omololu Omotosho ya bayyana cewa Najeriya ka iya fadawa rikici kan furuci da Aisha, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi idan ba’ayi hankali ba.

KU KARANTA KUMA: Wani kansilan arewa ya rarraba wa manoma kyautar takin zamani

Ya ce: “Karda uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari, ta yi amfani da dabbobi a matsayin sunaye gurin bayyana ‘yan Najeriya da shugabanninsu.

“’Yan Najeriya na son shugaban kasa mai lafiya, suna yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari fatan alkhairi, sannan bazasu so ganin shugabanni sun yi amfani da mulki gurin hallaka kasar ba.

“A 2015 ‘yan Najeriya, sun zabi canji ne, ba wai wasan siysa mara karewa dake kewaye da lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari ba."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel