Saura ƙiris na auri ɗiyata, saboda tsabar yawan ýaýana – Inji mai ýaýa 100

Saura ƙiris na auri ɗiyata, saboda tsabar yawan ýaýana – Inji mai ýaýa 100

- Yawan jama'an Duniya sun kai biliyan 7 da miliyan 500

- Wani mutumi mai shekaru 80 ya haifi yaya 100 cif cif

A yau ne ake bikin ranar kididdigar jama’a na Duniya, inda aka kiyasta jama’an Duniya sun kais u biliyan 7 da miliyan dari biyar.

Shafin BBC Hausa ta kawo labarin wani mutumin kasar Ghana mai suna Kofi Asilenu, wanda ya haifi yaya dai dai har guda 100 cif cif, kuma yace shi fa ba zai tsaya da haihuwa ba, don har yanzu bai gaji ba.

KU KARANTA: Anyi musayar wuta tsakanin yan fashi da Yan sanda a titin Zaria-Kano, an kashe 2

Shi dai wanna mutumi Kofi mai shekaru 80 mazaunin kauyen Amankrom ne dake kusa da babban birnin Ghana,Accra, kuma a nan yake zaune da iyalinsa gaba daya su dari cur, tare da mata 12.

Saura ƙiris na auri ɗiyata, saboda tsabar yawan ýaýana – Inji mai ýaýa 100

Mista Kofi da yar jaria

Kofi ya bayyana ma majiyar NAIJ.com cewa shi manomi ne, kuma shekarun yayan nasa su 100 na tsakanin 11 ne zuwa shekaru 50.

Saura ƙiris na auri ɗiyata, saboda tsabar yawan ýaýana – Inji mai ýaýa 100

Mista Kofi tare da yayansa

Kofi yace dalilin daya sa yake haihuwar yara da yawa shine saboda bashi da yan uwa, don haka yana bukatar wadanda zasu yi ma hidima idan ya mutu , sa’annan yace ciyar da yayan nasa ba wani matsala bane a gare shi, domin a baya shi mai kudi ne.

Saura ƙiris na auri ɗiyata, saboda tsabar yawan ýaýana – Inji mai ýaýa 100

Kofi mai ýaýa 100

Sai dai a yanzu yace wasu daga cikin yayansa dake aiki ne ke taimaka sa a yanzu wajen kulawa da iyalin nasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel