Amurka ce ke samun ribar rikicin da ke faruwa a Saudiyya

Amurka ce ke samun ribar rikicin da ke faruwa a Saudiyya

A zaman da ministocin harkokin wajen kasashen da suka yanke alaka da Qatar wato Saudiya, Masar, UAE da kuma Bahrain suka gudanar a Masar a ranar Laraba da ta gabata, sun sanar da cewa ba su gamsu da amsar da Qatar ta ba su a kan bukatu 13 da suka mika mata ba.

Wannan ne yasa suka sanar da cewa za su dauki matakai na gaba a kan kasar ta Qatar, wadda suke zarginta da daukar nauyin kungiyoyin 'yan ta'adda, daga cikin kungiyoyin kuma har da Hamas da kuma Muslim Brotherhood da ke da babban mazauninta a Masar, duk kuwa da cewa ministocin wadannan kasashe ba su bayyana matakai na gaba da za su dauka a kan Qatar ba, amma dai sun ce matakan za su shafi lamurra na siyasa, tattalin arziki musamman, duk kuwa da cewa yanzu haka wadannan kasashe sun yanke alaka da Qatar tare da rufe dukkanin hanyoyi na sama da kasa da kuma ruwa da suka hada su da kasar ta Qatar.

Amurka ce ke samun ribar rikicin da ke faruwa a Saudiyya

Amurka ce ke samun ribar rikicin da ke faruwa a Saudiyya

Wani abin da ke jawo saka ayar tambaya dangane da wannan mataki da wadannan kasashe 4 suka dauka a kan Qatar shi ne, yadda a zaman ministocin harkokin wajen nasu a Masar, suka bayyana cewa dole ne sai Qatar ta yi aiki da dukkanin abubuwan da aka cimmawa a zaman Trump da sarakuna da shugabannin larabawa a Riyadh, wanda kuma babban abin da taron ya cimmawa shi ne kafa rundunar kawance ta larabawa tare da hadin gwiwa da Isra'ila wajen yaki da Iran, duk kuwa da cewa an rubuta bayanin bayan taron ne tsakanin Trump da Saudiyya, wadda Muhammad Bin Salman matashi dan shekaru 31 ke tafiyar da ita a halin yanzu, inda sauran sarakuna da shugabanin da suka halarci taron sai dai suka ji ana karanta jawabin bayan taron ba tare da an shawarce su kan yadda za a rubuta bayanin da kuma abubuwan da zai kunsa ba, amma kuma ba su da wani zabi illa dole su amince da abin da aka cimmawa tsakanin Trump da Saudiyya.

Amurka ce ke samun ribar rikicin da ke faruwa a Saudiyya

Amurka ce ke samun ribar rikicin da ke faruwa a Saudiyya

To sai dai a nata bagaren Amurka wadda take da cikakken iko a kan Qatar da ma dukkanin kasashen da suka yanke alaka da ita, har yanzu taki daukar wani mataki na sasanta su, duk kuwa da cewa za ta iya yin hakan idan ta ga dama a cikin kyaftawa da bismillah, domin kuwa dukkaninsu suna kokarin burge ta ne da kuma neman kara tabbatar da biyayyarsu a gare ta, wanda hakan ya sanya masana ke ganin cewa akwai wata maslaha da Amurka take da ita a cikin wannan rikici da ake yi a tsakanin Saudiyya da kawayenta, da kuma Qatar a daya bangaren.

KU KARANTA: Za'a daina shigo da shinkafa ga baki daya - Audu Ogbeh

Babban abin da ke kara tabbatar da hakan shi ne, a zaman da kwamitin kula arkokin waje na majalisar dokokin Amurka ya gabatar a makon da ya gabata, dan majalisar dokokin Amurka Khokan Castro daga jam'iyyar Democrat ya tambayi wakiliyar Amurka a majalisar dinkin duniya Nikki Haley cewa, me yasa matsayin Amurka kan rikicin larabawa da Qatar yake karo da juna? Inda Amurka taki bayyana ma duniya matsayinta kana bin da ke faruwa sai dai ta ce matsala ce ta larabawa a tsakaninsu, alhali tana da iko a kansu baki daya? Sai Nikki Haley ta amsa da cewa; hakika wannan rikicin wata babbar dama ce ga Amurka domin ta yi matsin lamba a kan dukkanin bangarorin biyu.

Babban abin fahimta daga wannan furuci na babbar wakiliyar Amurka a majlaisar dinkin dinkin duniya Nikki Haley shi ne, Amurka za ta ci gaba da tatsar Saudiyya da Qatar a lokaci guda, tare da nuna ma kowane bangare cewa tana tare da shi kuma tana goyon bayansa, inda za ta ci gaba da tsorata Saudiyya da cewa Iran ce babban hadari a gare ta, dole ne ta kawo kudi a bata makamai domin ta kare kanta daga Iran, a daya bangaren kuma za ta rika tsorata Qatar da cewa Saudiyya ce barazana a gare ta, dole ne ta kawo kudi a bata makamai domin ta kare kanta daga Saudiyya da kawayenta, wanda hakan ke nuni da cewa ba abin mamaki ba ne ya zama cewa Amurka ce ma da kanta ta kitsa wannan rikici a tsakaninsu, domin ta yi ta tatsar daruruwan biliyoyin daloli daga bangarorin biyu, kamar yadda kuma shi ne hakikanin abin da yake faruwa a halin yanzu.

Da dama daga cikin masana harkokin siyasar kasa da kasa sun yi imanin cewa, rikici tsakanin Saudiyya da Qatar ba batun kafa kungiyoyi.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel