Wani kansilan arewa ya rarraba wa manoma takin zamani kyauta

Wani kansilan arewa ya rarraba wa manoma takin zamani kyauta

- Wani kansila ra rarraba wa manoman mazabarsa taki kyauta

- Gambo ya bukaci manoman da su yi amfani da takin don bunkasa samar da abinci

- A watan Mayu da ta gabata kansilan ya bada tallafin sukolashif ga daliban makarantun sakandare 53 a mazabar

Mista Danjuma Gambo, wani memba na kwamitin wucin gadi na karamar hukumar Kokona a jihar Nasarawa, ya rarraba wa manoma a cikin mazabarsa taki kyauta don bunkasa aikin noma da kuma samar da abinci ga mutanen yankin.

Gambo dan jam’iyyar APC mai mulki, wanda ke wakiltar mazabar unguwar Nikoro ya rarraba buhun taki guda 22 ga manoman a yau Talata, 11 ga watan Yuli a Kokona.

Kansilan ya bukaci manoman da su yi amfani da takin don bunkasa samar da abinci da kuma inganta zamantakewa da tattalin arziki a jihar.

A jawabin nasa, Mista Bala Adamu, shugaban kwamitin rarraba taki, ya yaba ma kansila ga tallafin.

KU KARANTA: Kwakwamba ta kashe yara 5 ‘yan gida daya a Cross River

Ya shawarci sauran ‘yan siyasa a mazabar da kuma jihar baki daya da su yi koyi da irin wannan alheri.

NAIJ.com ta tuna da cewa a ranar 23 ga watan Mayu, kansilan ya bada sukolashif ga daliban makarantun sakandare 53 a mazabarsa inda kowane dalibi ya samu 3, 000.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel