Anyi musayar wuta tsakanin yan fashi da Yan sanda a titin Zaria-Kano, an kashe 2

Anyi musayar wuta tsakanin yan fashi da Yan sanda a titin Zaria-Kano, an kashe 2

- Anyi bata kashi tsakanin yan fashi da yansanda a jihar Kaduna

- Jami'an Yansanda sun hallaka yan fashi biyu tare da illata sauran

Yan fashi guda biyu sun gamu da ajalinsu a yayin wani barin wuta da suka yi da jami’an rundunar Yansanda a kan babban titin hanyar Zaria zuwa Kaduna, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kaakakin hukumar Yansandan jihar Kano Magaji Musa Majiya ne ya bayyana haka inda yace wannan lamari ya faru ne a ranar Litinin 10 ga watan Yuli da misalin karfe 9 na dare a lokacin da yansandan suka hange su a kusa da garin garun Malam.

KU KARANTA: Wani mutum yayi ma matan aure su 7 fyaɗe a Katsina bayan ya asirce su

Majiya yace a lokacin da yan fashi suka hangi yansandan sai suka bude musu wuta, nan da nan Yansandan suka mayar da wuta, suka hallaka mutane 2 daga ciki tare da raunata sauran.

Anyi musayar wuta tsakanin yan fashi da Yan sanda a titin Zaria-Kano, an kashe 2

Yansanda

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito yansandan sun kwato makamai da suka hada da bindigar revolver, alburusai guda 12 da layu.

Daga karshe ya bukaci jama’a dasu taimaka ma jami’an yansanda da bayanai akan duk wani mutumin da basu gane take takensa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan kungiyar asiri sun hallaka wasu a legas, kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel