An harbe wani ma’aikacin NTA a jihar Edo

An harbe wani ma’aikacin NTA a jihar Edo

Rahotanni sun kawo cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari ga wani ma’aikacin gidan talbijin din Najeriya wato NTA mai suna Lawrence Okojie sannan suka harbe shi har lahira a garin babban birnin jihar Edo a ranar Asabar 8 ga watan Yuli.

Rahoton ya kuma nuna cewa an harbi mamacin ne bayan ya sauka daga bas na ma’aikatan NTA sannan kuma bayan y agama zantawa da matar sa a wayar salula inda yake shida mata da cewa ya kusa karasowa gida.

Sai dai matar ta sa ta ji shiru bayan ta dauki tsawon sa’o’I tana jiransa, sannan ta sake kiran layin wayarsa amma bata same shi ba.

Wannan ne ya sa ta nemi daya daga cikin abokan aikin sa a waya sannan suka dukufa neman maigidan nata.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya amince da Alkalai 19 na Kotun Masana'antuOsinbajo ya amince da Alkalai 19 na Kotun Masana'antu

A yayin da suke gudunar da bincike ne suka tsinci gawarsa a babban asibitin Benin.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda jihar Edo, Moses Nkombe ya tabbatar da faruwan al’amarin, inda ya kara da fadin cewa an kama wani mutum wanda ake zargi yana da hannu a cikin kisan.

Ya ce jami’an ‘yan sanda suna nan suna gudunar da bincike akan al’amarin domin gano wadanda suka aikata wannan mummunan ta’asar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel