Wani Sarkin Yarbawa yayi kira a sauya tsarin Kasar nan

Wani Sarkin Yarbawa yayi kira a sauya tsarin Kasar nan

- Wani Sarkin Yarbawa ya marawa shirin garambawul baya

- Alafin na Oyo yace dole ayi gyara idan ana so kasar ta cigaba

- Sarkin yayi wannan bayani ne wajen kaddamar da wani littafi

Wani Sarki na kasar Yarbawa watau Alafin na kasar Oyo ya nuna goyon bayan sa na ayi wa Najeriya garambawul idan ana so kasar nan ta cigaba.

Wani Sarkin Yarbawa yayi kira a sauya tsarin Kasar nan

Sarki Alafin na Oyo yace dole ayi gyara a kasar

Sarki Lamidi Adeyami yake cewa Gwamnatin Aguiyi-Ironsi ce ta fara rushe tsarin kasar wanda ake tafiya a kai a lokacin wanda hakan ya kawo wata matsalar. Sarkin yace ana murkushe wasu Yankin a tsarin da ake tafiya a kai.

KU KARANTA: Kungiyar Arewa tace ba ta goyon Buhari

Wani Sarkin Yarbawa yayi kira a sauya tsarin Kasar nan

Arewa na mana wayau Inji Sarkin Yarbawa

A cewar Sarkin dai Kasar Arewa ke wawushe mafi yawa arzikin kasar ganin irin yawan kananun Hukumomin da ke Jihohin. Mai martaban yace Gwamnatin Tarayya ke karbe kusan duk abin da sauran Jihohi su ka hada ta rabawa wasu Jihohin da ba su tabuka komai ba.

Wasu da dama dai su na kira ayi wa Kasar garambawul idan har ana so a cigaba. Kungiyar Afenifere ta zargi Arewa da hana ruwa gudu a Kasar nan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kai ziyara ga iyalan wasu da aka yi wa illa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel