Kwakwamba ta kashe yara 5 ‘yan gida daya a Cross River

Kwakwamba ta kashe yara 5 ‘yan gida daya a Cross River

Tashin hakali da ba’a sa masa rana, wani al’amari mai cike da al’ajabi ya afku a wani kauye mai suna Amana dake karamar hukumar Obanlikwu na jihar Cross River, bayan yara guda biyar ‘yan gida daya sun mutu sanadiyar cin kwakwambar da aka noma a gonar mahaifiyar su.

A cewar rahoto, mahaifiyar yaran ta bar masu kwakwambar su ci sannan ita ta tafi gurin taron wani biki.

Da kammala cin kwakwambar sai kawai yaran suka fadi matattu, dukkan su biyar din maza biyu da kuma mata uku.

Ana dai zargin cewa an sanya ma yaran guba a cikinta kafin su ci.

KU KARANTA KUMA: Wani masanin littafin injila ya yi ikirarin cewa an kirkiri labarin Yesu Almasihu ne don a mulki talakawa

Mai magan da yawun ‘yan sandan jihar, Irene Ugbo ta tabbatar da faruwar wannan al’amari, sai dai ta ce basu kama ko mutum daya ba izuwa yanzu.

Ta bayyana ma jaridar Daily Post cewa tuni jami’an yan sanda suka zunduma bincike a kan al’amarin.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel