INEC tayi magana game da korar Dino Melaye daga Majalisa

INEC tayi magana game da korar Dino Melaye daga Majalisa

– Kotu ta tuntubi Hukumar INEC game da batun Sanata Dino Melaye

– Hukumar INEC tace sai tayi nazari kafin ta dauki wani mataki tukun

– Wasu Lauyoyi na ganin cewa dole INEC ta dakatar da shirin

Hukumar INEC ta tabbatar da cewa wani babban Kotun kasar nan ta tuntube ta game da shirin yi wa Sanata Dino Melaye na Yammacin Jihar Kogi kiranye.

INEC tayi magana game da korar Dino Melaye daga Majalisa

Kwanakin Dino Melaye a Majalisa sun kusa zuwa karshe

Mai magana da bakin Hukumar Rotimi Oyekanmi ya tabbatar da wannan ba da dadewa ba amma fa yace ba hakan nan Hukumar zaben za ta tsaya da shirin na ta ba. INEC tace dole ta zauna ta fahimci hukuncin na Kotu.

KU KARANTA: APC za tayi wa tsarin mulkin kasa gyara

INEC tayi magana game da korar Dino Melaye daga Majalisa

Watakila Hukumar INEC za ta koro Dino Melaye

Hukumar dai tace ba za ta yi aiki da gaibu ba don haka sai tayi nazari game da hukuncin da babban Kotun Tarayya a Abuja ta yanke. Sai dai wani kwararren Lauyan Sanatan Mike Ozekhome yace dole Hukumar INEC ta dakata da shirin na ta.

Duk da umarnin Kotu Hukumar ta tasa Sanatan a gaba don har an fitar da jadawalin tantance kirayen da ake shirin yi wa Sanatan na barin Majalisar Dattawa.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda Gwamnan Osun ya ciri tuta

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel