Siyasa: Rikici ya balle a jami'iyar APC

Siyasa: Rikici ya balle a jami'iyar APC

- Ya kamata Odigie ya sauka daga kujerar sa

- Kai ne ka janyo mana rashin nasara

- Timi Frank ya bayyana ra'ayin shi

Rikici ya tashi a jam'iyar APC ta jihar Osun sanadiyar rashin nasarar da dan takarar jami'yar yayi a zaben ranar asabar ne sanata me wakiltar yammacin jihar akan dan takarar jami'yar PDP.

Mataimakin shugaban sakataren rahotannin na jam'iyar APC, Kwamared Timi Frank, wanda a yanzu haka shine mukaddashin shugaban sakataren saboda dakatarwa da jam'iyar tayi mishi wa shugaban, ya bayyanawa manema labarai cewa shugaban jam'iyar APC Chief John Odigie-Oyegun ne ya janyo musu wannan rashin nasarar a zaben jihar Osun.

Frank yace ya kamata ace shugaban jam'iyar ya sauka daga shugabancin jam'iyar saboda rashin nasarar da jam'iyar tayi, amma ya san cewa ba ze ajiye ba. Yace Adeleke, wanda ya bar jami'yar tasu saboda ganin irin yadda ake gudanar da mulkin jam'iyar, ya koma jam'iyar PDP kuma ya dawo ya ci zaben sanatan Osun, yace wannan abu da me yayi kama.

Siyasa: Rikici ya balle a jami'iyar APC

Siyasa: Rikici ya balle a jami'iyar APC

Timi ya cigaba da kawo korafe-korafen sa, yace lallai APC tayi abin kunya, don bai kamata ba a ce gwamnan jihar Osun dan jam'iyar APC bane, kuma ace dan takarar sanatan jihar na jam'iyar ya kasa cin zabe a jihar ba.

KU KARANTA: Cristiano ya fasa barin Kungiyar real madrid

Ya kuma kara da cewa, saboda rashin kulawar shugaban jam'iyar Odigie ne ya janyo rikicin jihar Kogi da wadansu jihohin. Ya kuma bada goyon bayan shi akan cewa idan har cancantar kiranye ne to Dino Melaye bai cancanya ba, sai dai shugaban jam'iyar tasu.

A karshe mukaddashin shugaban sakataren yake kiran mukaddashin shugaban kasa Osinbajo da yayi kira domin a kawo karshen wannan matsaloli da suke faruwa a jam'iyar. Yana kuma baiwa gwamnonin APC shawara akan su tashi tsaye su shige gaba domin a warware wannan matsalolin don matukar aka tafi a haka, shekarar 2019 za a ji ba dadi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel