Mun wuce lokacin rabuwa - Orji Uzor kalu

Mun wuce lokacin rabuwa - Orji Uzor kalu

- Tsohon Gwamnan Jihar Abia Dr Orji Ozu Kalu ya nuna rashin jin dadinsa akan wa’adin da aka ba iyamurai na barin Arewa

- Kungiyan matasan Arewa sun bawa yan kabilar Ibo wata uku da su bar yankin Arewa

Lokacin da Kalu ke ma shugaba Buhari adua ya samu lafiya. Yace ba a bun da zai hana shi yin wa’azin zaman lafiya Najeriya. kasa daya ce kuma na kowa da kowa ne.

Najeriya ta wuce lokacin da za ta rabe saboda duka kabilun sashen kasan suka hadu suka zama abun da ake kira Najeriya a yau.

Yan Nigeria sun dade suna zaman lafiya da junansu .Yakamata ayi duk abin da zai ja hadin kan yan kasan. Kalu ya fadi haka yayin da yake hira da manema labarai na Nigerian news agency (NAN).

Mun wuce lokacin rabuwa - Orji Uzor kalu

Dr Orji Uzor kalu

Tsohon gwamnan Abia kuma jigo a jami’yyar APC yace babu dan siyasan kwarai da zai so kasan ta rabe.

Ku Karanta:https: Jihar Kaduna ta zata fara gudanar da zabe da na'ura

Kuma yace yakamata duk mai fada aji a kasar yayi kokarin ganin kasan ta zama daya.Yace zai cigaba da kiran mutane zuwa ga akidan Nigeria daya da ganar da jama'a kyakawar halayen shugaba Muhammadu Buahri.

Yakara da cewa Buhari zai dawo cikin koshin lafiya kuma zai cigaba da ayyukan masu kyau da ya fara.

Yayi kira da babar murya akan samun kotu mai zaman kanta a kasan ,saboda hakan zai kara karfaffa zarta da sharia a mai kyau a kasan

Duk lokacin da aka samu matsala tsakanin fadar shugaban kasa da ta wakilai kotu za ta iya warware matsalan cikin sauki da yi ma kowa adalci.

Orji Ozu kalu yayi kira da yan Najeriya da su daina zagin shugaba Buhari. Abin da shugaban keso shine goyan bayan jama’a da addua

Buhari yana iya kokarin dan ganin kasan ta gyaru.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel